<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>68</hymn_number>
<title>Ya Ubangiji Yesu, Mun Taru Wurinka LW68</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Ubangiji Yesu, mun taru wurinka, Tunanin mutuwarka sun cika zukata.
 Mun ji muryarka Yesu, &quot;Gurasan nan ku ci,
 Raina ne da na bayar don tunawa da ni.&quot;

[V2]
 2) Ta wurin ikon Allah, kai farin haihuwa ne,
 Mu kuma za mu tashi mu zauna wuri ɗaya. Alkawarinka Yesu, ƙoƙon da muka sha,
 Jininka ne ya sayi rai na har abada.

[V3]
 3) Ƙaunarka, Mai Cetonmu, ta wuce saninmu,
 Tunanin raɗaɗin da ka sha dai dominmu.
 Yanzu kuwa cikin Sama addu'a ka ke yi.
 Ka riƙe mu, ya Yesu, mu ƴan Ekklesiyarka. Amin</lyrics>
</song>